Tsaro a Matakin Hukuma: Hukuma Da Mahukunta a Zamfara 2015-2019

     Tsakure

    Hukuma (wato gwamnati) ita ce ƙashin bayan al’umma a duniya, domin duk ƙasar da ba ta da hukuma da ke kula da tsarin rayuwarta da al’amuran harkokinta na yau da kullum; ta kauce hanya. Haka kuma wannan ƙasa ko gari za a iya cewa sun taɓe sun shiga ruɗu na rashin sanin alƙiblar da suka dosa. Wannan bincike zai yi tsokaci ne kan irin gudummuwar da hukumar jihar Zamfara ke bayarwa wajen kula da tabbatar da tsaro da ya shafi mutane ko al’ummar da ke cikin jihar, dangane da irin faɗace-faɗacen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma. Wannan hali ya haifar da matsalolo iri-iri ta hanyar kashe-kashen rayuka, ta’addanci da garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa ya zama ruwan dare. Hukuma ta bayar da gudummuwa don ganin ta warware waɗannan matsalolin da suka addabi jama’a ta hanyar kafa kwamitin kulawa da harkan tsaro a jihar, wanda ya samar da hanyoyi da dama da za a bi a magance waɗannan matsaloli da suka bijiro a wannan jihar ta Zamfara.           

    Fitilun Kalmomi: Zamfara, Tsaro, Hukuma, Mahukunta, Zaman Lafiya

    DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.020 

    Click HERE to download the complete article.

    Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture

    author/Abdullahi, M. and Sarkin Fada, I.

    journal/Tasambo JLLC | 20 Dec. 2022 |  P. 185-188

    pdf-https://drive.google.com/file/d/1c4SU2xHLczdlAz5IAFGtxukCDIBuTJFU/view?usp=share_link

    paper-https://drive.google.com/file/d/1c4SU2xHLczdlAz5IAFGtxukCDIBuTJFU/view?usp=share_link