Tsakure
Babbar manufar wannan bincike ita ce nazartar littafin Gogan Naka domin fito da hikimomin da marubucin ya yi amfani da su wajen jan hankalin mai karatu ko manazarci. An ɗora wannan bincike a kan ra’in hanyar nazari ta gargajiya ( Traditional Approach). An keɓance binciken a kan littafin Gogan Naka. Tushen bayani na biyu da binciken ya yi aiki da shi shi ne rubuce-rubucen masana da suka jiɓanci wannan bincike. Binciken ya tabbatar da cewa marubuci na iya cusa hikimomi da fasahohinsa a lokacin da yake ƙulla tunaninsa yayin rubuta littafinsa. Bisa ga haka, takardar ta tabbatar da bankaɗo salailan da marubucin ya yi amfani da su a cikin littafinsa tare da taurarin da ya cusa a cikin wannan littafi.
Fitattun Kalmomi: Gogan Naka, Tarke, Nazari
DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.021
author/Suleiman, M. & Usman, H.S.
journal/Tasambo JLLC | 20 Dec. 2022 | P. 189-198
pdf-https://drive.google.com/file/d/1jN3vIfgZNz1eb0I4Ohuxu5XnVpI4U06o/view?usp=share_link
paper-https://drive.google.com/file/d/1jN3vIfgZNz1eb0I4Ohuxu5XnVpI4U06o/view?usp=share_link