Nazarin Sauye-Sauyen Wasulan Karin Harshen Katsina Da Maraɗi

    Tsakure

    Bincike ya nuna cewa, harshen Hausa na da kare-kare masu yawa, daga cikinsu har da Karin harshen Katsinanci Bello (1962). Kazalika, a karin harshen Katsinanci, Sakamakon yawan al’umma da ke amfani da shi da kuma faɗin ƙasa da Katsinanci ya mamaye ana da hasashen cewa akwai ƙananan kare-karen harshe, ciki har da karin Maraɗi. Domin tabbatar da haka an yi amfani da hanyar tattara bayanai ta ganawa da lura ta ƙwaƙƙwafi domin samun bayanan da za su tabbatar da haka. Haka kuma, an yi amfani da ra’in tsarin sautin tsirau wajen tantance bayanan da aka samu kamar yadda Chomsky da Halle (1968) suka yi amfani da shi a littafinsu na (Sound Pattern of English) (S.P.E). Kamar yadda aka yi hasashe da farko binciken ya tabbatar da cewa, an samu sauye – sauye tsakanin karin harshen Katsinanci a birnin Katsina da na birnin Maraɗi a wasu wurare da suka haɗa da sauyawar baƙi da wasali, saƙala sauti, shafe ƙwayar sauti, musayar gurbi, kore raunanar baƙi, kore ganɗantawa da kuma kore hanɗantawa. A wannan takarda an yi ƙoƙarin kawo sauye-sauyen da suka shafi wasulla.

    Fitilun Kalmomi: Karin Harshe, Walwalar Harshe, Harshen Rukuni, Wasula

    DOI:  www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.016

    author/Haruna, A., Idris, Z.B. & Yankara, M.M.

    journal/Tasambo JLLC | 15 June 2023 |  P. 143-151

    pdf-https://drive.google.com/file/d/1IMFtn5AVbBKLllQZnfnDGGLQVEF8Tqev/view?usp=sharing

    paper-https://drive.google.com/file/d/1IMFtn5AVbBKLllQZnfnDGGLQVEF8Tqev/view?usp=sharing