Nazari a Kan Sauye-Sauyen Ɗafi a Cikin Jam’in Kalmomin Yara

    Tsakure

    Samuwar harshe na ɗaya daga cikin abubuwan ban mamaki na hallitar Ubangiji ga ɗan Adam. Haka ya sa aka himmatu ga nazarin yadda yara da manya ke sarrafa harshensu ta hanyoyi daban-daban. Jam’i a harshen Hausa yana ba da gagarumar gudunmuwa a harshen, domin ta hanyarsa ne ake tantance tilo, sannan ta hanyarsa ne ake gane ƙimarabu da adadi. Haka kuma, Jam’i ya kasance abu ne da ake aiwatar da shi yau da kullum. Domin da wuya a yi magana ɗaya ba tare da an aiwatar da shi ba. Manufar wannan maƙala ita ce nuna yadda yara sukan tsara jam’insu a harshen Hausa. An bi matakai na haƙiƙa wato zahiri wajen hanyar gudanar da wannan bincike wato wajen sauraron yara yayin furucinsu, ko kuma faɗin kalma, su kuma su ba da jam’inta gwargwadon fahimtarsu. An yi amfani da ra’in’Emergantism theory’ wato ra’i ne na ‘Machwinneys ’(1989) wanda ya yi nazari a kan harshen Ingilishi da Jamusanci, a inda ya nuna yadda yara suke sauye-sauyen ɗafi a jam’insu a tsakiyar kalma ko a ƙarshen kalma a waɗannan harsunan. Sakamakon bincike ya gano cewa, yara da ke a matakin shekaru takwas zuwa tara sukan tsara jam’insu a kan kuskure, ba tare da la’akari da sun yi daidai ba, ko akasin haka, domin kuwa su a wajensu daidai ne.

    Fitilun Kalmomi: Walwalar Harshe, Jam’i, Ɗafi, Hausar Yara

    DOI:  www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.015

    author/Salima Suleiman Isah

    journal/Tasambo JLLC | 15 June 2023 |  P. 134-142

    pdf-https://drive.google.com/file/d/1fhf5gjCFL_nsmT7L0RfCLV65MpirETxi/view?usp=sharing

    paper-https://drive.google.com/file/d/1fhf5gjCFL_nsmT7L0RfCLV65MpirETxi/view?usp=sharing