Nazarin Tubalan Salon Magana Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    Tsakure: 

    Amfani da ƙarangiya a cikin waƙoƙin baka na Hausa wani salo ne na nuna gwanintar harshe. Makaɗa Sa’idu Faru yana daga cikin irin mawaƙan da suke yin amfani da irin wannan salo don haka ne wannan muƙalar ta yi nazarin yadda makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da wannan salo a cikin waƙoƙinsa. Manufar wannan muƙala ita ce yin nazarin kalaman ƙarangiya a waƙoƙin Sa’idu Faru tare da bayyana sautukan da mawaƙin yake amfani da su domin ƙulla ƙarangiya a waƙoƙinsa. An yi amfani da dabarar sauraren waƙoƙimsa da nazarce-nazarcen masana a matsayin hanyoyin da aka bi domin tattara bayanan da aka yi amfani da su a wannan muƙala. A ƙoƙarin cimma manufa, an yi amfani da mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya wacce ta bayyana hanyoyin da ake nazarin yadda ake nazarin waƙar baka bahaushiya. Wanda ya jagoranci wannan mazhaba shi ne Farfesa Sa’id Muhammad Gusau. Bayan kamala wannan muƙala, an an lura da da cewa Makaɗa Sa’idu yana amfani da ƙarangiya don nuna gwanintar harshe da kuma yin zambo a cikin waƙoƙinsa.

    Fitilun Kalmomi: Ƙarangiya, Sautuka, Ƙalubale

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.013

    author/Hassan Rabeh & Nuhu Nalado

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 13