Da Tsohohuwar Zuma Ake Magani: Matakan Tsaro Na Gargajiya A Fagen Magance Matsalolin Tsaro A Zamfara

    Tsakure

    Daular Zamfara tana ɗaya daga cikin daulolin ƙasar Hausa da wasu masana suka ce tana cikin ‘banza bakwai’. Daga wani sashe na tsuhuwar daula ne aka sami jihar Zamfara. Jihar tana nan a yankin arewa maso yamma na arewacin Nijeriya. Zamfara ƙasa ce niimtacciya ta ɓangaren noma da ma’adinai na ƙarƙashin ƙasa. Akwai koguna da ƙoramu da suka ratsa jihar. Wannan ne ya sanya ake samun fadamu jefi-jefi a wasu sassa na jihar. Akasarin al’ummomin wannan jiha manoma ne da makiyaya. Shekaru aru-aru da suka shuɗe, manoma da makiyaya na Zamfara suna zaune lami lafiya tsakaninsu da junansu. A wannan zamani da muke ciki, zaman lafiya da amince wa juna ya ƙaranta a tsakanin manoma da akasarin su Hausawa ne da kuma makiyaya da mafi rinjayensu Fulani ne. Tsaro ya yi matuƙar taɓarbarewa a jihar sakamakon rashin jituwa tsakanin waɗannan al’ummomi. Wannan ya sa har ake samun sace-sacen dabbobi da kashe-kashe a tsaninsu musamman ma mazauna karkara. Wannan muƙala ta ƙuduri anniyar yin waiwaye na bin diddigin ayyukan magabata dangane da tsaro a Bahaushiyar al’ada da kuma duba a kan yadda har yanzu ake amfani da su a wasu wurare da nufin samun tsaro. Ra’in da za a gina muƙalar a kai shi ne Bahaushen ra’in da ke cewa, ‘Da Tsohuwar Zuma Ake magani.’ Tunanin wannan muƙala shi ne cewa, watsi tare da kauce wa bin matakan tsaro na gargajiya da aka saba da su kuma suka biya buƙatun tsaro ya taimaka sosai wajen haifar da wannan tayar da zaune tsaye da ake samu a jihar. Wannan ya sanya muƙalar yin waiwaye kan matakan tsaron na gargajiya da nufin zaƙulo yadda za a yi amfani da su a matsayin ‘tsohuwar zuma’ da za a iya amfani da ita wajen magance matsalar tsaro a wannan zamani. Za a yi haka ne ta hanyar tattaunawa da waƙilan tsaro masu ruwa da tsaki kan lamarin tsaro da ma waɗanda shaidi abubuwan da ke faruwa dangane da lamarin. Muƙalar ta gano cewa kasawar hukuma da kuma al’umma haɗe da daina bin wasu matakan gargajiya ne suka haifar da taɓarɓarewar tsaro don haka a sake maido tare da ƙara inganta matakan tsaro na gargajiya domin inganta tsaro.

    Fitilun Kalmomi: Matakan Tsaro, Tsaro, Gargajiya, Zamfara, Zaman Lafiya

    DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.014

    author/Gummi, M.F. and Kurawa, H.M.

    journal/Tasambo JLLC | 20 Dec. 2022 |  P. 125-137

    pdf-https://drive.google.com/file/d/1nOJsnkHz0Hpv0YDtcEXdnOXT3SJBr6xG/view?usp=share_link

    paper-https://drive.google.com/file/d/1nOJsnkHz0Hpv0YDtcEXdnOXT3SJBr6xG/view?usp=share_link