Tsakure
Marubuta waƙoƙin siyasa na Hausa kan yi amfani da basirar da Allah ya yi musu wajen yin amfani da sarrafa harshe cikin hikima domin su jawo hankulan jama’a zuwa ga manufa. Aminu Ibrahim Ɗandago shi ma na ɗaya daga cikin irin waɗannann marubuta da Allah ya horewa wannan. A wannan nazari an kalli yadda marubucin ya yi amfani da dabarar sarrafa harshe a waƙar Ba Na Shakka ta ANPP. An ɗora wannan nazari bisa Mazahabar Abdulƙadir Ɗangambo (2007) ta Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Dabaru da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan nazari sun hada da tattaunawa da marubucin an kuma samo matanin waƙar daga hannun marubucin kai tsaye a kuma rubace. A binciken kuma an gano marubucin ya yi mafani da dabarar sarrafa harshe ta hanyar aron kalmomin Ingilishi da Larabci da Fulatanci da kalmomin Hausa masu sabuwar ma’ana karin harshen Kananci da ƙari a cikin kalma da kuma maganganun hikima irinsu: karin Magana da habaici da kuma zambo. Gudunmawa da binciken ya bayar ita ce, ƙara bada haske ga manazarta da ɗalibai ta yadda za su nazarci sarrafa harshe a rubutacciyar waƙa, musamman a ɓangaren waƙoƙin siyasa ta fannin adabin Hausa.
Fitilun Kalmomi: Sarrafa Harshe, Waƙa, Salo
DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.022
author/A'ishatu Isma'il Adamu
journal/Tasambo JLLC | 20 Dec. 2022 | P. 199-207
pdf-https://drive.google.com/file/d/1AjB1jwI6nFu8zZB0dHu9jHQErFNRdCqE/view?usp=share_link
paper-https://drive.google.com/file/d/1AjB1jwI6nFu8zZB0dHu9jHQErFNRdCqE/view?usp=share_link