Gudummawar Sarakuna Wajen Bunƙasa Ilimi a Nijeriya Ta Arewa

  Tsakure

  Kafin tsarin mulkin dimokuraɗiyya, al’amarin ilimin al’umma ɗungurungum a hannun sarakuna yake. Bunƙasar ilimi ko komabayan hakan ya taallaƙa ne ga jajircewar sarki da muƙarrabansa a wannan fannin. Ƙudurin wannan maƙala shi ne leƙa fagen tarihi domin zaƙulo irin rawar da sarakunan Arewa suka taka wajen ilmantar da al’ummar wannan yankin ta fuskar ilimin zamani (boko) da na addinin Musulunci. Kadadar nazarin ta taƙaita ne tsakanin 1905 zuwa 1966. An ɗora shi bisa tsarin binciken laburare (library research) inda aka zaƙulo bayanai daga kundatattun fayil-fayil da wallafe-wallafe. Binciken ya gano cewa, sarakunan wancan lokaci sun yi namijin ƙoƙari wajen kafa ingantaccen tushen ilimi ta fuskokin da suka haɗa da nuna goyon baya da bayar da tallafi. Haka kuma, takardar ta bayar da shawarwarin da suka haɗa da nuna yadda ɗaukar hannu daga wannan ƙoƙari na mazan jiya zai iya samar da sauyi mai nagarta ga lamarin ilimi.

  Fitilun Kalmomi: Ilimi, Sarakuna, Ƙasar Hausa

  DOI:  www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i01.012

  author/Adamu Rabi’u Bakura & Abu-Ubaida Sani

  journal/Tasambo JLLC | 15 May 2023 |  P. 98-106

  pdf-https://drive.google.com/file/d/1ptAiCiHz1mFJTOI5R6H9tEBchgqJ5khN/view?usp=share_link

  paper-https://drive.google.com/file/d/1ptAiCiHz1mFJTOI5R6H9tEBchgqJ5khN/view?usp=share_link