Tsakure
Sadarwa wata hanya ce ta isar da saƙo ko bayanai daga wani zuwa wani. Saboda haka
sadarwa yanayin sarrafa bayanai ne tsakanin al’umma cikin tsari da
hikima. A wannan takarda an yi tsokaci a kan rawar da ‘yan jarida ke takawa
wajen fito da sunayen ‘Yan ta’adda musamman a jihar Zamfara inda ayyukansu ya
fi shafuwa. Manufa a nan ita ce, tabbatar da wanzuwar kalmomin da ‘yan jarida
ke amfani da su a yayin yayata ayyukan masu ta’addanci da faɗakarwa a kafafen watsa labarai kama daga rediyo da talabijin har zuwa ga
kafafen sada zumunta irin su intanet WhatsApp da facebook da ire-irensu. Bugu
da ƙari, dubarun da aka
yi amfani da su wajen gudanar da wannan bincike sun haɗa da; zantawa da ‘yan jaridu na kafafen watsa labarai daban-daban da suka
haɗa da; gidan talabijin na ƙasa da ke Gusau (NTA Gusau) da gidan rediyo da
talabijin na jihar Zamfara da rediyon FM na ƙasa da ke jihar Zamfara da gidan talabijin na
Gamji Gusau da gidan rediyon BBC Hausa da ke London. Sakamakon binciken da aka
fito da su sun haɗa da; samar da
wannan nau’in Hausa na da nasaba da faɗakarwa ga mutane da ire-iren sunayen da ake kiran wannan rukunin mutane
domin ankara daga sharrinsu.
Fitilun Kalmomi: Ta’addanci, ‘Yan Ta’adda, ‘Yan Jarida, Zamfara
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i01.020