Tarbiya a Falsafar Al’ada

      Tsakure

    Al’ummar Hausawa sun daɗe suna gudanar da harkokin rayuwarsu kamar yadda al’adarsu ta tanada. Kowace al’umma haka ake sa ran takasance tana alfahari da al’adunta. Tarbiya tana daga cikin daɗaɗɗiyar al’adar Hausawa wadda ta yi tasirin gaske a zukatansu. Bahaushe mutum ne mai zurfin tunani, wanda yake tsayawa ya ƙirƙiro wa kansa abin da zai amfane shi a tsawon rayuwarsa a duniya. Don haka sai ya samar wa kansa hanyoyin tarbiyantar da ‘ya’yansa a al’adance kafi zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa. Hanyoyinsun haɗa da tatsuniyoyi da labaran hikima da hikayoyi da camfe-camfe da sauransu. Wannan hikima ta taimaka wajen hana yara aikata wani abu da ya saɓa wa al’adar mutanen da ake Magana a kansu. Ta yi ƙoƙarin kawar da miyagun al’adu waɗanda suka saɓa wa koyarwar al’adun Hausawa. Ta kyautata zamantakewa da biyayya ga iyaye da shugabanni da barin wasu miyagun ɗabi’u da al’ada ta kyamata, kafi zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa. Haka kuma addinin musulunci ya taka rawa wajen gyara halaye da ɗabi’u na rashin tarbiya da al’adar Hausawa ta yi hani da aikatasu. Kamar rashin biyayya ga iyaye da rashin girmama manya da shugabanni da sata da zina da sauran halaye marasa kyau. Dalilin haka ya sa wannan takarda za ta yi tsokaci a kan tasirin da addinin musulunci ya yi wajen kyautata kyawawan ɗabi’u da halaye na gari da al’adar Hausawa ta horas kuma aka tarbiyantu da su. Haka kuma mu dubi yadda baƙin al’adu suka gurɓata tarbiyar ‘ya’yan Hausawa musamman a kan shaye-shayen muyagun ƙwayoyi da sauran abubuwa na rashin ɗa’a. 

    Fitilun Kalmomi: Al’ada, Tarbiyya, Zamantakewa

    DOI:  www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.026

    author/Aliyu Rabi’u Dangulbi

    journal/Tasambo JLLC | 15 June 2023 |  P. 214-218

    pdf-https://drive.google.com/file/d/19hCpYUEmPbGs9FhUqLgff7JBFC5nW3SB/view?usp=sharing

    paper-https://drive.google.com/file/d/19hCpYUEmPbGs9FhUqLgff7JBFC5nW3SB/view?usp=sharing