Hannu Ba Ka Da Tsoro: Gurbin Hannu Cikin Tunanin Masu Abu “Hausawa”

    Tsakure

    Tunanin wannan bincike shi ne, fayyace yadda sunan hannu ya yi naso da malkashi cikin tunanin Bahaushe da ke bayyana cikin adabinsa, da al’adunsa, da harshensa. Binciken da aka yi na take da kirarin da Bahaushe ke yi wa hannu, na cewa ba ya da tsoro. An yi amfani da kayayyakin adabi da al’ada da harshe domin tabbatar da dugadugan bincike. Karance-karancen ayyukan magabata kawai ba zai warkar ba, dole sai an haɗa da yawon rangadi da tattauna na rukunin mutane daban-daban. Da aka fahinci babu wani aiki bugagge ko wani ba shi ba da aka yi a kan Bahaushen tunani kan hannu sai aka kwakkwahe takardun rubutu. An ɗora wannan ‘yar takarda bisa fasula (13) haɗe da gabatarwa da naɗewa. Takarda ta yi wa hannu karatun ƙwaƙƙwafi bayan fayyace suna (2) na hannaye, ta sake ƙwalailaice abubuwa (15) da ke liƙe ga hannun ɗan Adam da sunayen da Bahaushe ya laƙaba musu. A jimlace an leƙo amfanonin hannu (23) tare da fayyace nau’o’in rabe-raben hannu (9) a Hausance, An kafa hujja da sassan adabi (23) da suka ambaci hannu a mahanga mabambanta, tare da amfani da ɗiyan waƙa (7) na mawaƙan baka daban-daban domin kwakkwahe bayani. Labaran raha (2) aka yi garkuwa da su na tabbatar da samuwar shawagin hannu cikin tunanin Bahaushe. A jimlace an sarrafa haujjoji (81) da suka tabbatar da da’awar wannan bincike. A kan haka, binciken ya hango sakamako (5) da aka rairaye cewa, babu wata gaɓa daga cikin gaɓɓan ɗan Adam da ta kai hannu tasiri cikin tunaninsa. Don haka ya zama jagora daga cikin gaɓɓan ɗan Adam. Tabbas! Yadda Bahaushe ke kallon bahagon hannu haka nan yake a addinance da kimiyance. A kan haka ne wannan takarda ke da fahintar ya kyautu a saka nazarin sassan gaɓoɓin jikin ɗan Adam cikin manhajar koyarwar harsunanmu. Akwai buƙatar mayar da himma ga wannan fanni na nazari.

    Fitilun Kalmomi: Hausa, Hausawa, Al’ada, Hannu

    DOI:  www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.012

    author/Aliyu Muhammad Bunza

    journal/Tasambo JLLC | 15 June 2023 |  P. 106-114

    pdf-https://drive.google.com/file/d/1BZLI2ljWu2598J96x6o8olZxy8tEKSVd/view?usp=sharing

    paper-https://drive.google.com/file/d/1BZLI2ljWu2598J96x6o8olZxy8tEKSVd/view?usp=sharing