Daga Hausar Rukuni Zuwa Ɓoyayyiyar Al’ada: Keɓaɓɓen Nazari A Kan Hausar Telolin Garin Gusau

  Tsakure

  Wannan bincike ya ta’allaƙa ne kan nazarin Hausar teloli. Manufar binciken shi ne nazartar ire-iren kalmomi da jimloli da teloli ke amfani da su ta hanyar ba su ma’anonin da suka bambanta da maganar yau da kullum. Kadadar binciken ta taƙaita a garin Gusau da ke jahar Zamfara. An yi amfani da tattaunawa a matsayin babbar hanyar tattara bayanai. A bisa haka ne aka yi hira da teloli daban-daban da ke garin Gusau. Binciken ya gano cewa, akwai kalmomi da jimloli daban-daban da telolin ke amfani da su waɗanda suka bai wa ma’anonin da suka bambanta da na gama-gari. Waɗansu kuwa sukan kasance ƙirƙira ce kai tsaye. Binciken ya kalli wannan a matsayin wani abinci a fagen nazarin harshe da al’ada. Kundace su da nazartar su mataki ne na bunƙasa harshe tare da taskacewa da daidaita al’ada musamman yayin fito da tasirin amfani da iren-iren waɗannan Hausar ta rukuni ga zamantakewa.

  Fitilun Kalmomi: Telololi, Hausar Rukuni, Harshe, Al’ada

  DOI:  www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.013

  author/Abu-Ubaida Sani & Sani Adamu

  journal/Tasambo JLLC | 15 June 2023 |  P. 115-123

  pdf-https://drive.google.com/file/d/1RtIgDazYufyBMRYE3rYthIJcsEPxzxHl/view?usp=sharing

  paper-https://drive.google.com/file/d/1RtIgDazYufyBMRYE3rYthIJcsEPxzxHl/view?usp=sharing