Tsakure
Wannan muĆ™ala an nazarci walwalar harshen Hausa a Turai. Kamar yadda aka sani, harshe abu ne da yake da walwala, don haka ne ma yakan iya aro daga wani harshen zuwa wani, ko kuma a samu bambance-bambancen lafazi daga wani rukuni na al’umma ko nahiya da suke amfani da harshe É—aya. Don haka, muĆ™alar ta gano akwai hargitsa-ballen Faransanci da Hausa inda aikin ya kira irin wannan yanayi da Farausa. Haka kuma, an sami hargitsa-balle na Jamusanci da Hausa a nan kuma aka samu Jamausa hakazalika, an samu Ingausa da Arabsa. da ake samu a sakamakon haÉ—a Hausa da Ingilishi a lokaci guda da kuma haÉ—a Hausa da Larabci. Daga Ć™arshe aikin ya Ć™irĆ™iro sababbin kalmomi da ya kira su da Jamausa da Farausa kamar yadda ya gabata a baya.
Fitilun Kalmomi: Arabsa, Jamausa da Hargitsa-Balle
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.022