Tsakure
Wannan makala ta yi nazari a kan rayuwar Hausawa
a zamantakewarsu da kazar Hausa. Tunanin wannan maƙala ya samo asali ne daga duban irin
yadda Bahaushe ya shaƙu da kiwon kaza zamunna da yawa, da yadda sunanta ya samu
matsayi a wasu sassan adabin baka. Maƙalarta kuma hango
cewa ko bayan sassan jama’a, akwai wasu abubuwa kamar dabbobi da tsuntsaye da
tsirrai da ke da muhimmanci a cikin muhallin Bahaushe wanɗanda zumuncinsu da al’umma na da tasiri da matsayin da ya
kamata a yi nazari. Manufar wannan ita ce yin amfani da wasu sassan adabin
Hausa a fito da wani sashe na falsafar rayuwa da al’adu da zumunci a tsakanin
Bahaushe da kazar Hausa. Daga cikin hanyoyin da aka yi amfani da su domin cimma
manufar wannan bincike akwai tattaunawa da jama’a da duba ayyukan masana da
tattaro maganganun azanci da wasu bayanai na adabi masu alaƙa da aiki kai tsaye a cikin al’ummar
Hausawa. An kuma yi amfani da Ra’in
Nazarin Al’adu daga adabin baka (Cultural Studies Theory) wanda ya ba da dama
tsauro bayanan al’ada daga adabin baka ta hanyar yin la’akari da yanayin
rayuwar al’umma da tattalin arziki da tsarin zamantakewa da yadda suka yi
tasiri a rayuwar al’umma. Wannan ya ba bincike tsakuro bayanai game da adabin
baka da ƙunshiyarsa da kuma
wasu al’adu da ɗabi’u da suka shafi rayuwar Hausawa dangane da
dangantakarta da kaza. Sakamakon bincike ya tabbatar da cewa akwai zumuncin
zamantakewa tsakanin al’ummar Hausawa da wasu tsuntsaye kamar kaza wanda
tasirin ya haifi wasu nau’o’in adabin bakan Hausa masu bayanin wasu al’adu da ɗabi’un Hausawa.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.040
author/Dr. Nasiru Aminu & Dr. Rabi’u Aliyu Rambo
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 40