Tsakure
Samar da tsaro shi ne
babban lamarin da al’umar Zamfara suke buƙata
a yau. Rashin tsaro ya
dami kowa da kowa, babu yaro babu babba, ya game birane da ƙauyuka. Saboda haka, a wannan maƙala mai taken ‘Nazarin Kalmomin Ta’addanci a Wasu Waƙoƙin Baka,’ an yi ƙoƙarin
fitowa da kalmomin ta’addanci da mawaƙa ke amfani da su a yayin rera waƙoƙinsu. Manufa a nan ita ce, fitowa da muhimmiyar rawa
da waɗannan kalmomi ke takawa wajen bunƙasa harshen Hausa, ta hanyar nuna
gwaninta da ƙwarewa
da kuma iya sarrafa harshen Hausa da mawaƙa da su. Dubarun da aka yi amfani da su wajen
gudanar da wannan bincike shi ne, kawo baitocin waƙa daga waƙoƙi
daban-daban da kaurara kalma mai nuni da ta’addanci da bayanin yanayin ƙirarta da kawo ajin kalmar da kuma sharhi
a kan muhallin da kalmar ta fi dacewa ta zo a tsarin jumla. Ra’in da aka yi amfani
da shi wajen gudanar da wannan maƙala
shi ne, ra’in dangantakar harshe da rikici (Language of
Violence) na Smith, Alison G. da wasu (2008). Bugu da ƙari, binciken ya fito da sakamako da suka haɗa da; tabbatar da rukunin kalmomin
ta’adanci a harshen Hausa da kuma rawar da suke takawa a ɓagaren ilmin walwalar harshe.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Kalma, Ta’addanci, Waƙar Baka
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.041
author/Isah Sarkin Fada
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 41