Tsakure
Adabin baka wani babban kundin tarihi ne, da kowane irin tarihi sai ya
dafi kafaɗarsa za a ga
zatin tsawonsa. Tunanin wannan ɗan bincike, taskace gudunmuwar dabbobin ƙasar Hausa
ga haɓaka Bahaushen Adabi. Binciken ya zaɓi kura a matsayin karan gwajin dahi. An tattaro kayan
aikin bincike guda tamanin da uku (83) da aka samo cikin kundayen bincike,
wallafaffun ayyuka, hira, da tattaunawa, da rangadi, ta ga-ni-ga-ka, da ta
waya, da hanyoyin sadarwa na WASAP da TES, da Yanar Gizo. Bayan tsettsefe
bayanai aka ɗora takardar
a kan fasula (20) da suka haɗa da gabatarwa da naɗewa. An tsara kayan aikin da aka tattaro cikin rukuni
tara (9). Rukunin nahawu an samu misalai (6), karin magana (20), tatsuniya (1),
wasan yara (1), tarihi da tarihihi (6) labaran gargjaiya (3), an kuma gayyato
mawaƙan baka (8) da aka sarrafa ɗiyan waƙoƙinsu (14). An tattaro sassan magungunan gargjaiya (4),
da dabarun tsaro na gargjaiya (4), duk masu alaƙa da
gudunmuwar kura a adabinmu. An gwada tsawon kura da dabbobi (18) na gida da
daji a falsafar adabin bakan Bahaushe.
Waɗannan kayan
aiki (83) su suka ba mu damar yanke hukuncin cewa, lallai adabin baka ƙololuwar
falsafar al’umma ce, da sai da shi, za a iya fahintarsu, da ƙyallaro
tunnaninsu. Binciken ya tabbatar da; daga cikin dabbobin ƙasar Hausa,
babu wadda tasirin ta ya yi zara cikin Bahaushen Adabi kamar kura. Ɗabi’un kura
munana sun rinjayi kyawawansu a duniyar adabin Bahaushe. A ƙarshe,
binciken ya zartar da hukuncin naɗa wa kura rawanin sarautar TAURARUWAR BAHAUSHEN ADABI. Ta tabbata
matsoraciya ce, amma ban tsoronta ya fi tsoronta yawa. Tunanin Bahaushe a kan
hanya yake: “Kura ga tsoro ga ban tsoro”.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.022
author/Aliyu Muhammadu Bunza
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 22