Biki na Farar Kaza...: Nazarin Farin Ciki da Godiyar Aliyu Nata a Waƙar Aurensa Ta “Na Gode”

  Tsakure

  Nazarin waƙar “Na Gode” ta Aliyu Nata ya tattauna batutuwa ne a kan farin ciki da godiyar mawaƙin, saboda irin yadda ‘yan uwa da abokan arziki suka amsa gayyatar da aka yi musu a lokacin aurensa. Maƙalar ta yi tsokaci a kan godiyar Allah daga waƙar, sannan ta yi magana kan lokacin da mawaƙin ya yi godiya da alaƙar godiya da lokaci sai kuma tsokaci kan sosuwar zuciya a godiya. Nazari ya kawo tarihin mawaƙin da taƙaitacciyar bita a kan waƙar baka da nagari da kuma godiya. Manufar yin wannan nazari ita ce, a tarke godiya da farin ciki daga waƙar auren Aliyu Nata domin a gano irin murnar da ya yi da kalaman da ya yi amfani da su da kuma yadda ya sarrafa su. Binciken ya zavo waƙar “Na Gode” daga cikin waƙoƙin Aliyu Nata saboda waƙa ce da take ɗauke da murnar cikar dogon gurin mawaƙin na yin aure kuma waƙar tamkar ƙanwa ce ga waƙarsa ta “Aure Martaba” bakandamiyar Aliyu Nata. Masu bincike sun shifci waƙar da aka nazarta, suka tantance ɗiyanta tare da gudummuwar mawaƙin, an nemi tarihin mawaƙin kuma ya turo da bayanai gwargwado ta WhatsApp, sannan binciken ya sarrafa ɗan waƙa goma a misalai da ya kawo daga waƙar “Na Gode”. A dunƙule, maƙalar ta gano godiya a Hausa tana da faɗin gaske, abu ne da ke da alaƙa da girmamawa da yabawa da nuna murna da sauransu. Uwa-uba, faɗin Alhamdu lillahi kai wa maƙura ne a godiya ga Allah (S.W.T.), hakan yana da alaƙa da neman ƙarin ni’ima a wurinsa kuma sunkuyawa ce da miƙa wuya ga mai duka. Binciken ya gano ban gajiyar da mawaƙin ya yi na cike da farin cikinsa, inda tarbiyyarsa ta bayyana a waƙar. Godiya da farin cikin mawaƙin na da nasaba da lokaci da sosuwar zuciya, kuma ɗiyan waƙar na ƙunshe da hotancin zucin mawaƙin game da yadda taron aurensa ya gudana. Godiyar Aliyu Nata tana fatar ɗorewar zumunci da abokan zumuncinsa kamar yadda a Hausa, “Na gode!” na nufin, idan mutum ya sami dama zai yi alheri fiye da wanda aka yi masa.

  Muhimman Kalmomi: Aliyu Nata, Aure, Biki, Farin Ciki, Gayya, Godiya, Waƙar Baka ta Yau

   DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.023

  author/Ayuba, A. & Bugaje, H.M.

  journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 |  Article 23