Nazarin Turke a Waƙoƙin Wasu Makaɗan Asharalle na Jihar Katsina

  Tsakure

  Wannan nazari ya ƙunshi taƙaitaccen bayani a kan waƙar Asharalle ne da kuma tsokaci a kan turakun waƙoƙin wasu makaɗan Asharalle na Jihar Katsina. An yi amfani da ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) ne wajen gina wannan nazari tare da fito da wasu turaku a waƙoƙin wasu makaɗan asharalle na jihar Katsina ta amfani da ra’in, waɗanda suka haɗa da: Turken yabo da na ta’aziyya da na zambo da na koɗa kai da na faɗakarwa da na siyasa da kuma na soyayya. Haka kuma an gina muradin wannan nazari ne domin gano yadda makaɗan Asharalle suke amfani da fasaharsu wajen gina turakun waƙoƙinsu. Ginshiƙan hanyoyin da aka bi wajen aiwatar da wannan bincike su ne; tattaro bayanai da matanonin waƙoƙin makaɗan Asharalle, inda aka tattaro wasu waƙoƙin makaɗan Asharalle, waɗanda aka saurare su kuma aka juye su a rubuce. Haka kuma an tattaro bayanai ta hanyar hira da wasu makaɗan Asharalle. Haka kuma, nazarin ya ba da gudummawa wajen fito da hikimar da makaɗan Asharalle suke amfani da ita yayin gina turakun waƙoƙinsu.

  Fitilun Kalmomi: Turke, Makaɗan Asharalle, Waƙar Baka Bahaushiya (WBB)

  DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.038

  author/Musa Abubakar Kurawa

  journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 |  Article 38