Kwatancin Karin Maganar Hausa Da Manganci Ta Fuskar Jigo

  Tsakure

  Manganci wani yare ne da wata kabila ke amfani da shi wajen sadarwa, masu amfani da shi su ake cewa Mangawa. Ana samun su a yankin kasar Haɗeja da ke Jihar Jigawa. Sun cakuɗa da Hausawa matuka, wannan ya sa kusan al’adunsu da yanayin zamanakewarsu suke cuɗanya da juna. Domin akan sami auratayya da harkokin kasuwanci da ma sauran al’amuran gudanar da rayuwa da juna. Saboda haka a ɓangaren harshe da adabi, ba abin mamaki ba ne domin an sami kamanceceniya a azancin magana da yadda ake amfani da aron kalmomi wa juna. Irin wannan ta sa ake samun haɓakar adabi, a ɓangaren karin magana ta fuskar jigonsu a waɗannan harsuna mabambantan juna. Yin hakan kuma yana kara bunkasa harshe da adabi tare da nuna alaka da juna, sannan kuma da fito da muhimmancin zaman lafiya da al’ummun ke da shi. A wannan takarda an nazarci Karin maganganun Hausawa da Mangawa ne ta fuskar jigon tarrbiyya, musamman abin da ya shafi haƙuri da juriya da neman na kai wato sana’a. An kwatanta Karin maganganun an gano suna da kamanceceniya da juna ta fuskar jigoginsu.

  Keɓaɓɓun Kalmomi: Hausawa, Mangawa, Karin Magana, Jigo, Tarbiyya, Haƙuri, Juriya, Sana’a

  DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.037

  author/ABDULKADIR, Ginsau PhD

  journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 |  Article 37