Tasirin Musulunci a Kan Auren Hausawa

  Tsakure

  Rarrabe tsakanin al’adun aure da Hausawa suka gada kaka da kakanni da abubuwan da addinin Musulunci ya ya zo da su, ba abu ne mai sauƙi ba. Idan aka lura da irin tasirin da addinin Musulunci ya yi a kusan dukkan ɓangarorin rayuwa, za a ga cewa wasu abubuwa da suka shafi aure sun sauya daga abin da al’ada ta zo da shi ya zuwa ga abin da addinin Musulunci ya zo da shi. Musulunci ya zo da dukkan tsare-tsare, kuma rashin bin wannan tsari na Musulunci, kan iya zama barazana ga auren ma’aurata da kuma rayuwarsu ta gaba ɗaya. Wannan takarda  na da manufar: bayyana auren Hausawa, ta kuma fito da tasirin Musulunci a kan auren Hausawa tare da haskaka alfanun Musuluncin a cikin auren Hausawa. Hanyar da aka bi wajen aiwatar da wannan bincike ta haɗa da hira da wasu mutane da karance-karancen littattafai da kundayen binjcike. An ɗora wannan maƙalar a kan ra’in Sauyin al’adu. Maƙalar,  ta fito da irin tasirin da Musulunci ya yi a wasu al’adun Hausawa na aure, tun daga kore wasu, sauya wasu, da kuma samar da wasu al’adun.

  Keywords: Al’ada, aure, Musulunci da tasiri

   DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.026

  author/Maikwari, H.U. & Lawan, M.S.

  journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 |  Article 26