Tsakure
Dabarun bayar da labari dabara ce da mawari ke
amfani da ita wajen warware labarinsa. Warwara kuwa mawari shi ne yake da dama wajen nuna Æ™warewarsa domin jan zarensa sala-sala ta yadda saÆ™onsa zai isa ga al’umma, kusan
mawara ƙwararru suna amfani da dabarun bayar da labari wajen
yin tasiri a cikin labaransu, kusan mafi yawan labaran suna ɗauke ne da dabarun bayar da labarai. Saboda haka wannan muƙala za a yi bakin gwargwado wajen fito da
hanyoyin da mawarin waÉ—annan labarai ya bi wajen gina
dabarun ƙulla habarcensa, haka kuma muƙalar za ta kawo wasu misalai na dabarun bayar da
labarai daga wasu labaran Magana Jari Ce.
Fitilun Kalmomi: Warwara, Salo, Zamani, Kwaikwayo
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.025
author/Ramatu Ishaq
journal/Tasambo JLLC | 15 February 2024 | Article 25