Homa Ko’ina Da Ruwanku: Laluben Sarkanci a Cikin Waƙoƙin Fada Na Makaɗa Sa’idu Faru

    Tsakure: 

    Sarkanci muhimmiyar sana’ar gargajiya ce. Irin ayyukan da masu aiwatar da sana’ar suke yi a cikin al’umma, sun haɗa da samar da kifi, wata halitta da ke ƙunshe da sanadarai masu inganta jiki da ƙara masa lafiya sannan ga gudunmuwar da suke bayarwa a fagen kiwon lafiya na gargajiya a al’ummar Hausawa. Waƙoƙin sarauta ko waƙoƙin fada, waƙoƙi ne da mawaƙan Hausa suke rerawa tare da kiɗa domin yabo da gwarzanta sarakunan ƙasar Hausa da nufin ƙwarzanta su da nishaɗantar da su tare kuma da yaɗa martaba da muhibbarsu ga duniyar Hausawa masu saurare da sha’awar waƙoƙin baka. Babban aikin Sarakuna shi ne mulki da jagorancin al’umma tare da ba su kariya da yi masu adalci. Aiwatar da sana’o’in gargajiya aiki ne da ya rataya a wuyan talakawa, amma duk da haka a cikin waƙoƙin sarauta na Hausa, ana samun jirwaye na wasu muhimman sanaoin gargajiya a cikin kalaman azanci a waƙoƙin makaɗan fada, ciki kuwa har da makaɗa Sa’idu Faru. Adabi madubi ne na rayuwar al’umma don haka ba abin mamaki ba ne idan waƙoƙin fada sun ƙunshi lamurran aladu na rayuwar al’umma. Ƙudurin wannan muƙala shi ne yin nazari a cikin waƙoƙin fada na makaɗa Sa’idu Faru da nufin zaƙulo lamuran da suka jiɓinci sarkanci ko kamun kifi a cikinsu. An tattaro waƙoƙin fada na makaɗa Sa’idu Faru da dama domin sauraron su a natse ta yadda za a fito da turaku daban-daban da suka danganci sana’ar sarkanci. Muƙalar ta gano dalilan da suke sa makaɗan fada saka lamarin sarkanci a cikin wasu waƙoƙinsu. Daga ciki akwai samun damar yin zambo da shaguɓe ga ‘ya’yan sarauta, tun ma ba a ce masu adawa da sarki ba. Haka ana saka batu da ya jiɓinci sarkanci domin a nuna alhairi da sarautar wanda ake wasawa ta haifar ga al’ummar da yake jagoranta, da sauran abubuwa makamantan waɗannan.

    Fitattun Kalmomi: Homa, Lalube, Sarkanci, Waƙoƙi, Fada

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.011

    author/Musa Fadama Gummi Ph.D & Abdullahi Sarkin Gulbi Ph.D

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 11