Tsakure:
Makaɗa
Sa’idu Faru yana ɗaya
daga cikin makaɗan
fada a ƙasar
Hausa. Ya yi wa sarakuna da ‘ya’yan saraki mabambantan waƙoƙi
a lokacinsa. Sannan yana daga cikin makaɗa
ko mawaƙan
da suke sassaƙa ƙananan saƙonni
a lokacin da suke ƙulla waƙa. Saboda haka, babbar manufar wannan
muƙala ita ce,
bayyana tubulan ginin turken da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen ƙulla waƙar da ya yi wa Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur, mai suna ‘Koma Shirin Daga na Bubakar, Gamda’aren Alƙali wan Maza’. An gudanar da wannan bincike ta hanyar karantawa daga bugaggun bayanai da sauraron wasu daga cikin waƙoƙin makaɗa
Sa’idu Faru. Bugu da ƙari, binciken ya gano cewa, tubulan ginin turken
da makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen ƙulla zaren tunanin waƙar sun haɗa da tubalin zumunci ko zumunta da tubalin zambo da
tubalin koɗa
kai da tubalin tarihi
da kuma tubalin habaici.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.010
author/Sani Hassan & Dr. Abdullahi Yakubu Darma
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 10