Muhammadu Macciɗo (Sarkin Kudu) a Bakin Makaɗa Sa’idu Faru

    Tsakure: 

    Wannan takarda ta fito da rawar da makaɗa Sa’idu Faru ya taka wajen iya yabo, wadda ta kai shi ga matsayi irin na manyan makaɗan sarakuna, har ma fiye da wasu. Ya zama gogaggen makaɗin Fada da ya ɗara saura saboda zalaƙarsa wajen iya zaɓen lafuzzan yabo ya gina waƙoƙin fada. An kawo wasu kalamai da lafuzzan da makaɗin ya yi matsayin tubalan yabon Muhammadu Macciɗo (Sarkin Kudu), waɗanda ba a samu wani makaɗi da ya faɗawa uban gidansa irinsu ba. Kalaman da lafuzzan sune suka zama mizanin da aka auna zalaƙa da basirar makaɗin wajen iya yabo. Daga cikin hanyoyin da aka bi, akwai bibiyar wasu waƙoƙin Muhammadu Macciɗo(Sarkin Kudu), aka kalato waɗannan misalai.

    Fiitilun Kalmomi: Sa’idu Faru, Muhammadu Macciɗo, Waƙar Baka, Kwarzantawa, Martabawa, Ɗaukakawa, Darajantawa, Kurantawa

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.022

    author/Halima Mansur Kurawa & Atiku Ahmad Dunfawa

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 22