Tsakure:
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sauraro. Da wannan ne ya sa fasihai kan dage su ga sun zaɓo salailan da za su dace da su, su kuma ba su dama su ga sun sace zuciyar masu sauraren su, domin ganin haƙarsu ta cim ma ruwa na neman samu karɓuwa ga abokan hulɗarsu. Salon jerin sarƙe (Parallelism) shi ne dabarar tsarawa da jera kalmomi ko jumloli iri guda a cikin ɗiyan waƙa da nufin jaddadawa ko ƙarfafawa ko nuna wata danganataka ko alaƙa a tsakanin gunduwoyin ɗiyan waƙa. Wannan maƙala ta ƙudiri aniyar zaƙulowa tare da nazartar salon jerin sarƙe daga cikin wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, inda za a bi wasu ɗiyan waƙoƙnsa a nuna yadda ya sarrafa salon, ta hanyar jerowa da tsara kalmomi da jumloli iri guda ko masu alaƙa da juna domin ya isar da wani saƙo. Maƙalar ta ginu ne a kan nau’in bincike bi-sharhi, inda aka zaƙulo wasu waƙoƙin makaɗin waɗanda ake ganin suna ƙunshe da salon jerin sarƙe a cikinsu, sannan a warware yadda ya ƙunshe tunanin nasa ta hanyar yin sharhi ga ɗiyan waƙoƙin. Maƙalar ta tattara bayanan da ta yi amfani da su ne ta hanyar bibiyar tahirin makaɗin da sauraron waƙoƙinsa domin ganin an tace waɗanda suke ƙunshe da wannan salo a cikinsu. Sannan kuma aka juye su a takarda. A ƙarshe maƙalar ta tabbatar da harsashenta na cewa waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru cike suke da salailai mabambanta, wanda salon jerin sarƙe ɗaya ne daga cikinsu, inda ta tabbatar da hakan ta hanyar kawo misalai na yadda makaɗin ya sarrafa salon, tare da yin sharhi a kan ɗiyan waƙoƙin nasa.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.021
author/Rabiu Bashir PhD
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 21