Tsakure:
Nazarin Falsafa a waƙar
baka na nufin zaƙulo wata hikima ta musamman wadda mawaƙi
ya yi amfani da ita a cikin waƙoƙinsa. Kasancewar Falsafa wata taska ce
matattara tataccen tunani da hasashe ko tsinkaya wadda yawanci haziƙan
mawaƙan Hausa kan yi amfani da ita domin
nuna hikima da hangen nesa a cikin waƙoƙinsu. Wannan takarda ta ƙunshi
fito da falsafa kai tsaye daga cikin wasu waƙoƙin
Malamin kiɗi mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba wato makaɗa Sa’idu Faru. An bi hanyar tattara waƙoƙin
tare da saurarensu ɗaya bayan ɗaya, kana aka tace waɗanda suka ƙunshi
irin kaifin tunanin mawaƙin (falsafa) daga ɗiyoyin waƙoƙinsa,
sannan kuma an tattauna da ma’abota sauraron waƙoƙinsa
domin neman ƙarin bayani na wasu kalmomin cikin waƙoƙin.
Wannan takarda an ɗora ta ne a kan Ra’in alfanun Sassan Al’umma wato
(Functionalism Theory) wanda ra’i ne da ya yi fice a wajen nazarin al’adu da
adabin al’umma wanda fitaccen masanin nan mai suna Charls Darwin (1809-1882) ya
samar, wanda ya yi aikin sa a kan alfanun sassan Halittu masu rai a fannin
dabbobi. Daga baya aka samu wasu Turawa masana tsarin zamantakewar al’umma suka
goya wa Charles Darwin (1809-1882)
baya. Su waɗannan Turawa kamar yadda Ado (2022) ya bayyana sun yarda da
cewa kowace al’umma tana da sassa daban-daban, kuma kowane sashe yana taimakawa
wajen ginuwar a’lumma. Daga cikin waɗannan magoya baya na Charles sun haɗa da; Emile Durkhein (1858-1917) da Herber Spencer (1820-1903) da Weber (1864-1920) da
sauransu. Hausawa al’umma ce cikakkiya kamar kowace al’umma ta Duniya da take
da nata tsarin na falsafa da sha’anin zamantakewa, kuma Hausawa suna da sassa
daban-daban ɗaya daga ciki su ne mawaƙan
baka waɗanda
suke tamkar ginshiƙi a cikin adabin al’ummarsu. Da wannan ɗan bayani ne ake ganin dacewar wannan
bincike da wannan ra’i. Bugu da ƙari wannan takarda ta ƙunshi
muhimman misalai na ɗimbin falsafar da ke cushe a cikin waƙoƙin
makaɗa
Sa’idu Faru tare da cikakken sharhi da bayanan da suka sawaƙa.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.024
author/Maryam Abubakar Ibrahim
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 24