Tsakure:
Kambamawa wata dabara ce ta mawaƙa inda suke faɗin wata magana fiye da yadda abin yake a rayuwa ta zahiri, domin su isar da wasu saƙonni. Manufar wannan takarda ita ce fito da wasu ɗiyan waƙoƙin Sa’idu Faru waɗanda suke ƙunshe da salon kambamawa tare da yin sharhi gwargwadon fahimta. An ɗora wannan aiki a bisa ra’in mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya wadda Gusau (2003 da 2015) ya assasa. An tattaro wasu matanonin waƙoƙin Sa’idu Faru ta hanyar amfani da Diwanin Waƙoƙin Baka na Gusau (2009), da kuma sauraron wasu waƙoƙin tare da rubuta matanoninsu a takarda. An gano cewa Sa’idu Faru yana amfani da salon kambamawa domin ya isar da wasu saƙonni, da kuma ƙara wa waƙa armashi domin jawo hankalin jama’a. Daga cikin saƙonni da Sa’idu Faru yake isarwa ta hanyar amfani da kambamawa akwai muhimmancin wasu kyawawan halaye kamar faɗin gaskiya da haƙuri da kyauta. Sannan kuma yana nuna matsayin wasu sarakuna da kuma nuna iyakoki da faɗin wasu masarautu na ƙasar Hausa.
Muhimman
Kalmomi: Waƙa,
salo, kambamawa, faruwar wani abu, faɗin ƙasa, kyawawan halaye
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.025
author/Bunguɗu, A.I., Rabi'u, S.A. & Abdulmalik, S.
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 25