Nazarin Turakun Waƙoƙin Masarautar Ƙauran Namoda na Makaɗa Sa'idu Faru

    Tsakure: 

    Wannan takarda an tsara ta ne da manufar fito da turakun da ke cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru na masarautar Ƙauran Namoda da ke Jihar Zamfara, Nijeriya. An yi wannan tunani ne saboda a ƙara fayyace gurbin da masarautar take da shi a daular Usmaniya, tare da matsayin masarautar a bakin Makaɗa Sa’idu Faru. Haka kuma, wannan ya ƙara tabbatar da basirar makaɗa Sa’idu Faru a ɓangaren makaɗan fada, musamman yadda waƙoƙinsa suke cike da turaku daban-daban. Domin nazarin ya cimma nasara, an yi amfani da hanyoyin bincike na sauraren waƙoƙin mawaƙin tare da nazartar ayyukan da aka gudanar rubutattu masu alaƙa da batun da ake nazari a kai. Kauce wa kwasar karan mahaukaciya ya sanya aka yi wa takardar kadada, inda aka taƙaita binciken ga waƙoƙin makaɗin guda biyu. Wato, waƙar Sarkin Ƙauran Namoda Abubakar Garba wanda ya yi mulki daga shekarar 1952-1960 da kuma ta Uban ƙasar Banga Sarkin yaƙi Sale Abubakar wanda ya yi mulki daga shekarar 1934-1963. Binciken ya yi amfani da Ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) wanda Gusau, (1993, 2003, 2008, 2011, 2014, 2015) ya assasa. Takardar ta yi ƙoƙarin fito da turaku bakwai a cikin waɗannan waƙoƙi guda biyu. Turakun da aka iya fitowa da su, su ne: Turken addini da yabo da koɗa kai da jarunta da kyauta da zuga da kuma roƙo. An kammala nazarin da bayyana sakamakon bincike waɗanda suka haɗa da, Masarautar Ƙauran Namoda tana cikin manyan masarautu da tarihin daular Usmaniya ba zai kammala ba idan ba a ji motsin ta ba. Turakun da ke cikin waƙoƙin Masarautar Ƙauran Namoda sun ƙara tabbatar da martaba da kuma buwayar masarautar a idon duniya. Haka kuma, Waƙoƙin Masarautar Ƙauran Namoda na Sa’idu Faru tamkar wata taska ce da ta adana tarihi da iyakokin masarautar da kuma matsayin masarautar a daular Zamfara da ma ta Usmaniya gaba ɗaya.

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.008

    author/Muhammad Arabi UMAR & Halidu Sanda ƘAURA

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 08