Nazarin Ararrun Kalmomi a Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo ta Sa’idu Faru

    Tsakure: 

    Makaɗa Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin makaɗan fadar da suke amfani da kalmomin aro wajen isar da saƙon da waƙarsu take ɗauke da shi a ƙasar Hausa. Ya yi wa sarakuna da ‘ya’yan saraki mabambantan waƙoƙi a lokacinsa. Sannan yana daga cikin makaɗa ko mawaƙan da suke zaɓen kalmomin da suke amfani da su wajen sassaƙa ƙananan saƙonni a lokacin da suke ƙulla waƙa. Saboda haka, babbar manufar wannan takarda ita ce, bayyana ararrun kalmomin da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen ƙulla waƙar da ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, mai suna Bajimin Gidan Bello Mamman na Yari, Sarkin Kudu Macciɗo ci Maraya. An gudanar da wannan bincike ta hanyar karantawa daga bugaggun bayanai da sauraron wasu daga cikin waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru. Bugu da ƙari, binciken ya gano cewa, makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da ararrun kalmomin da Hausa ta aro daga harshen Larabci da kuma Ingilishi wajen ƙulla zaren tunanin waƙarsa. Kalmomin da suka samo asali daga harshen Larabci sun haɗa da Duniya da Ilmi da Dalili da Allah da kuma Istingifari. Har wa yau, akwai kalmomi irin su Almuɗɗafa da Lahira da Wasicci da Azumu da kuma Sunna. Ararrun kalmomin da mawaƙin ya yi amfani da su na harshen Ingilishi kuwa, sun ƙunshi Bandur da Yadi da Fam da Biskit da Minti da kuma Sitawut. Haka kuma, akwai kalmomi irin su Lemu da Soda da Sigari da kuma Benci.

    Fitilun Kalmomi: Waƙa, Makaɗa Sa’idu Faru, Ararrun Kalmomi, Harshen Ingilishi, Harshen Larabci

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.009

    author/Dr. Abdullahi Yakubu Darma & Sani Hassan

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 09