Tsakure:
Ɗan waƙa shi ne ruhin duk wata waƙar baka ta Hausa. Ashe kan ɗan waƙa ya zama tamkar wata ma’ajiyar saƙonni ne, manya da ƙanana waɗanda suke fita daga zuƙatan makaɗan baka na Hausa, su kuma zuba su, tare da shirya su a cikin ɗan waƙa domin isarwa ga waɗanda abin ya shafi, wato su sadar da su ta hanyar rerawa da gwamawa da amon kiɗa. Manufar wannan bincike ita ce yin tarken tsarin ɗan waƙa da nau’o’insa a cikin wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Takardar ta yi nazari bisa matakan ƙulla ɗan waƙa na + Jagora + ’Y/Amshi + tunani + rauji + gaɓa +kalma + saɗara + G/waƙa + ɗa + ɗiya + kiɗa da Makaɗa Sa’idu Faru yake bi ya ƙulla nau’o’in ɗan waƙa guda uku. Wato gajeren ɗan waƙa mai ƙunsar kammalalliyar ma’ana da matsakaicin ɗan waƙa mai ƙunsar gutsire ko kammalalliyar ma’ana da kuma dogon ɗan waƙa mai kammalalliyar ma’ana. Kuma takardar ta ƙalailaice tsarin ma’ana ta duban sassauƙan A1 A2 A3-A4 da kuma tsattsauran ɗan waƙa A1-B1, C1, D1, E1, F1 G1-Z10 a cikin ɗaiɗaikun ɗiyan waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. An yi amfani da ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) na Gusau (1993. 2003, 2014 da 2023) a matsayin ra’in da aka ɗora wannan takarda a kansa. A wannan takarda an yi amfani da dabarar bincike ta bi-bayani, wato hanyar sharhantawa wajen yin sharhi da ƙalailaice ɗiyan waƙoƙin da aka zaɓa. Takardar ta gano cewa, baya ga ɗa mai sauƙi da mai tsauri, za a iya fitar da sabon rukunin ɗan waƙa, wato harɗaɗɗen ɗan waƙa. Haka kuma, ba sa samun saukar ma’ana a gajeren ɗan da dogon ɗan waƙa ta ɗa da ɗa, sai dai a tsakanin saɗaru. Amma ana samu a cikin matsakaicin ɗan waƙa.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.055
author/Muhammad Musa Labaran
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 55