Yanayi da Siffofin Gwarzaye a Waƙar Marigayi Hakimin Talata Mafara Sarkin Gabas Shehu Ɗan Sarkin Bauran Dange ta Makaɗa Sa’idu Faru

    Tsakure: 

    Babban maƙasudin wannan takarda shi ne nazarin siffofin gwarzaye a Waƙar Marigayi Hakimin Talata Mafara Sarkin Gabas Shehu Ɗan Sarkin Bauran Dange ta Makaɗa Alhaji Sa’idu Faru. Gwarzaye wasu ɗaiɗaikun mutane ne waɗanda mutane suke girmamawa da kuma tunawa saboda kyawawan ayyukansu da halayensu. Mutane ne da suke yin ayyukan sambarka da bajinta da buwaya da ɗaukaka. A wajen gudanar da wannan bincike an bi hanyoyin samun bayanai da suka haɗa da: tattaro waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru musamman waɗanda suka shafi wannan nazari; nazarin bugaggun littattafai da kundayen bincike da takardu na ilimi; tattaunawa da masana da manazarta adabi da harshe domin samun ingantattun bayanai. A wannan muƙala an gano makaɗa Alhaji Sa’idu Faru ya yi amfani da dabarar abuntawa da siffantawa da kamantawa da faɗin asali ko salsala wajen bayyana siffofin gwarzonsa a zubin ɗiyan waƙarsa ta Marigayi Hakimin Talata Mafara Sarkin Gabas Shehu Ɗan Sarkin Bauran Dange. 

    Muhimman Kalmomi: Siffofi, Gwarzaye, Waƙa. Abuntawa, Kamantarwa Siffantawa, Asali/Salsala

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.054

    author/Sani Bashir & Kabiru Abdulkarim

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 54