Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris

    Tsakure: 

    Waƙa wata hanya ce ta isar da saƙonni cikin salo mabambanta, wato ta baka ko rubutacciya.Waƙoƙin baka da rubutattu hanya ce mai   gamsarwa wajen isar da saƙo. A wannan maƙala, an yi ƙoƙarin bibiyar waƙar Sa’idu Faru ne makaɗan baka, kuma makaɗan fada, domin fito da irin hikima da fikira da zalaƙa da basirar da Allah ya ba shi wajen sarrafa harshe. A cikin wannan waƙa, makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da kwalliya da nuna darajar da Sarki yake ɗauka da shi, inda yake siffanta Sarkin Zazzau da wasu dabbobi masu daraja da ƙrfi da kwarjini. Haka kuma da danganta shi da gidan da ya fito na sarauta. Nazarin zai taɓo waƙar da Sa’idy Faru ya yi wa Sarkin da taƙaitaccen tarihin Sarkin da ire-iren kirarin da ake masa a wurare mabambanta. An bi hanyoyi da ya kamata da amfani da dabaru akan yi ƙoƙarin nemo waƙar ta Sarkin Zazzau da sauraronta; don zaƙulo bayanan da ake buƙata a waƙar, da kuma saƙon zuwa ga gaɓar da ake magana a kai. An yi ƙoƙarin ɗora wannan bincike a kan Ra’in mazahabar Nason Adabi a Al’adu (Folk – Cultural Theory) wanda William Bascom ya ƙirƙira, sannan kuma aka samu mabiya daga ƙasar Amurka waɗanda suka bunƙasa shi. Binciken ya ƙare da sakamakon da aka samu yayin gudanarwa.

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.042

    author/Musa Abdullahi

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 42