Tsakure:
Waƙar baka fasaha ce wadda take kallon
fanni na rayuwar Hausawa ciki kuwa har da yabo wanda yake kashin bayan duk wata
waƙar
baka ta sarauta. A binciken ilimi, yabo ba sabon abu ba ne a fagen nazari fanni
na al’ada da adabi musamman a waƙoƙin makaɗa
Sa’idu Faru, saboda irin yadda ya yi amfani da turken yabo cikin waƙoƙinsa
domin (kambama) Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo. Haka kuma an tsakuro tubalan ginin yabo a cikin waɗannan maƙoƙi. An ɗora
kayan cikin guɗanar
da wannan bincike don fito da manufa bisa hanyar dogaro na nasaba da kyauta da kuma kyakkyawan halaye da mawaƙin
ya yi wa
uban gidansa.
Tattaunawa da ziyarar gani da ido da karance-karancen litattafai da muƙalu
tare da sauran waƙoƙin makaɗa
Sa’idu Faru duk domin kwalliya ta biya. An yi amfani da mazhabar waƙar baka Bahaushiya, wadda Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau
ya ɗabbaƙa. Binciken ya yi
nasarar gano waƙar Saidu Faru ta Muhammadu Macciɗo cike take da yabo ta fuskar addini da kyauta da
kyawawan ɗabi’u na asalin
gidan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.041
author/Halima Adamu, Amina Abubakar & Samira Adamu Gurori
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 41