Tasirin Habaici a Waƙoƙin Sa’idu Faru Wajen Kare Martabar Sarki

    Tsakure: 

    Masarautun gargajiya gidaje ne masu daraja da ɗaukaka a idon al’ummar Hausawa da suka kamata a girmama su a kowane ɓangare na rayuwa. Makaɗa Sa’idu Faru ya taka rawa wajen ƙoƙarin kare martabar waɗannan gidajen sarautu ta hanyar amfani da habaici a cikin waƙoƙinsa na sarauta. Wannan muƙala mai suna ‘Tasirin habaici a cikin waƙoƙin Sa’idu Faru wajen kare martabar sarki”za ta yi magana ne a kan tasirin da habaici ya yi wajen kare martaba, da ɗaukaka darajar masarautar gargajiya ta Sarkin yaƙin Banga Sale Abubakar, a gundumar Ƙauran Namoda, a yankin Arewa Maso-Yamma. Domin cimma manufar wannan muƙala, an yi amfani da hanyar samo kaset-kaset na waƙoƙin Saidu Faru da ya yi wa Sarkin Yaƙin Banga, a lokacin rayuwarsa. Habaici magana ce da mawaƙan Hausa suke furtawa zuwa ga sarakuna abokan hamayya ko ‘ya’yan sarakuna ko fadawa ko wasu makaɗan sarakuna da suke adawa da sarkin da ake yi wa waƙa. Makaɗa Sa’idu Faru yana daga cikin makaɗan fada da suka taka rawar gani wajen kare martabar gidan sarautar gargajiya ta Banga ta hanyar amfani da habaici wajen faɗakarwa da ilmantar da sarki game da irin shirin da ‘ya’yan sarakuna da ‘yan adawa ko abokan hamayyarsa suke yi domin rushe martabar masarautarsa ko kuma gidan sarautar. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da wannan hanya ta habaici domin ya kare martabar sarautar gargajiya daga mugun nufin ‘yan adawa na ganin sun tarwatsa haɗin kai da sarki yake da shi tsakaninsa da ‘yan sarautar Banga. Muƙalar ta gano cewa, a cikin waƙoƙinsa da ya yi wa Sarkin Yaƙin Banga Sale Abubakar, Sa’idu Faru ya tabbatar da martabar wannan masarauta a idon duniya ta hanyar jawo hankalin jama’a su fahimci cewa ‘ya’yan sarakuna da abokan hamayya ba waɗanda za a ba amana ba ne. Koyaushe manufarsu su ƙulla wa sarki sharri da fatar ya mutu su gaje shi, su yi sarautar Sarkin Yaƙin Banga. Muƙalar ta gano cewa habaici dabara ce da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da ita wajen jawo hankalin sarki da masu saurare su fahimci cewa, manufofin ‘ya’yan sarakuna ko abokan hamayya ko fadawa ko sauran makaɗan fada zuwa ga masarautar gargajiya, gyara kayanka ne, wanda Hausawa ke cewa ba ya zama sauke mu raba.Sai dai wasu lokuta abubuwan da ‘yan adawa suke nunawa ga sarki ba wai don ƙiyayya ba ce, a’a, domin su ƙara tunatar da shi ne wajen gyara tafiyarsa ta hanyar yi wa talakawansa adalci ba tare da nuna banbanci ko son kai ba. Wannan dabara ta amfani da habaici ta ƙara ɗaukaka daraja da kwarjini da kare martabar Sarkin Yaƙin Banga a lokacin da yake mulki.

    Fitilun Kalmomi: Habaici, Sarautun Gargajiya, Martabar Fada, ‘Ya’yan Sarki, da Abokan Hamayya

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.044

    author/Aliyu Rabi’u Ɗangulbi & Idris Hamidu

    journal/Conference Proceedings | November 2024 |  Article 44