Tsakure:
Nazarin salo fanni ne da masana da manazarta suka daɗe suna bincike a kansa. Haka abin yake idan aka yi maganar nazarin salo a waƙoƙin Hausa. An sami masana irin su Yahya (2001) da Gusau (2003) da suka yi rawar gani wajen nazarin sa. Kodayake masu iya magana kan ce “ilimi kogi ne...” wannan ya sa aka zaɓi nazarin wani muhimmin fanni na salo a wannan maƙala, wato nazarin kwalliya a waƙoƙin Sa’idu Faru, sai dai muƙalar za ta taƙaita ne ga waƙa ɗaya tilo wadda sha-kudun ce idan dai a batun salo ne a waƙa. Manufar nazarin kuwa ba ta rasa nasaba da ƙara fito da baiwar da Allah ya yi wa wannan mawaƙi ta naƙaltar harshen Hausa da iya sarrafa shi a waƙa har a ce da wannan waƙa tubarkalla. An saurari wannan waƙa, tare da tarken salon kwalliya da ya fito a cikinta. An fahimci cewa Sa’idu Faru gwani na gwanaye ne wajen amfani da jinsi daban-daban na tsuntsaye da sauran halittu wajen sakaya ma’ana da adonta waƙa.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.045
author/Dr. Hauwa Muhammad Bugaje
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 45