Tsakure:
Karin Magana wani babban jigo ne
daga cikin rassan adabin bakan Bahaushe tun gabanin ya sadu da baƙin al’ummu a
duniya. Hakan ya sa ake samun tsarmin sa cikin magangannu yau da kullum a
tsakanin mutane har ma a cikin waƙoƙinsu. Dangane da haka, sanin waƙa sai ɗaliban nazari, domin kuwa, su ne ke da alhakin shiga waƙa don su tono
wasu asiran da ke cikinta. A dalilin hakan ne ya sa wannan nazari ya ƙudurci shiga wasu
daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru domin ya
lalubo irin yadda yake tsarma karin magana a cikin ɗiyan waƙoƙinsa., inda za a ga irin yadda yake kawo karin maganar kai tsaye ba tare ya
canza shi ba, ko ya yi luguden karin maganar, ko ya rage maganar, ko ya ƙirƙiro karin maganar
ko kuma ya yi takin saƙa da yadda ma’ana da tsarin amfani da karin maganar take.
Domin cimma nasarar hakan an yi amfani da dabarar sauraren wasu daga cikin waƙoƙinsa da himmar
taskace kutsen karin magana a waƙoƙin, a ƙarshe ana hasasshen takardar ta gano gurbin karin magana
wajen isar da saƙon a tafashen makaɗa Sa’idu Faru
Fitillun Kalmomi: Nazari, Karin Magana, Makaɗa, Saidu Faru
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.006
author/Dr. Abdullahi Sarkin Gulbi & Musa Abdullahi
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 06