Tsakure:
Masana suna la’akari da waɗansu alƙaluma yayin ayyana makaɗan Hausa a ƙarƙashin wani rukuni na musamman daga cikin tarin rukunonin makaɗa da ake da su a farfajiyar adabi da al’adun Hausawa. Waƙoƙin fada na daga cikin shahararrun rukunonin waƙoƙin baka. Wani abin lura shi ne, akan samu makaɗan da ke ƙarƙashin wannan rukuni da suke sauya sheƙa ko su kasance jemagu sakamakon tasirin zamani ko waɗansu dalilai masu alaƙa da tattalin arziki ko waninsa. Binciken nan yana da manufar bitar rayuwa da waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru domin ganin ko ya sauya sheƙa ko kuma ya kasance makaɗin sarauta kaifi ɗaya na tsawon zamanin kiɗansa? An yi amfani da dabarun ƙalailaice waƙoƙin makaɗin da kuma yin hira da masana a wannan fanni a matsayin hanyoyin tattara bayanai. Sakamakon binciken ya tabbatar da cewa, Sa’idu Faru ya tabbata makaɗin sarauta na yankan shakku, domin kuwa dukkannin waƙoƙinsa ba su fita daga da’irar sarauta da masarauta ba. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da nuna dacewar tattarawa da kundace waƙoƙin wannan shahararren makaɗi domin gudun salwantar su.
Fitilun Kalmomi: Kiɗa, Waƙa, Waƙoƙin Fada, Waƙoƙin Sarauta, Makaɗan Fada, Makaɗan Sarauta
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.005
author/Dr. Adamu Rabi’u BAKURA & Abu-Ubaida SANI
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 05