Tsakure:
Manufar wannan takarda ita ce, zaƙulo dubarun zambo da habaici kamar yadda suke ƙunshe a cikin wasu
ɗiyan waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru tare da nuna yawan aukuwarsu a cikin waƙoƙinsa. An yi amfani
da dabarar bincike ta saurare aka saurari wasu waƙoƙi bakwai (7), aka
kuma juyesu a takarda don tattara sakamakon bincike. An yi ƙoƙarin ɗora wannan bincike bisa ga ra’i na tarken Waƙar Baka Bahaushiya
(WBB) wato Gusau (2023) wanda Gusau ya fara ya samar 2003 ya jadadda a 2011,
2014 da 2015. Sai kuma ya sabunta shi a 2023. Haka kuma, Bahaushen Ra’i a wasu
wurare dai-dai gwargwadon fahimta. Saboda masana kamar su Bunza, (2018:2), Tudun
wada (2006), Malunfashi, (2014:50) da Koko (2011:3) a ruwaitar Ado, (2020) suna
ganin cewa: “Hikimomi da Fasahar Hausawa tana nan a karin maganganunsu. Don
haka, ana iya samar da ra’i a nazarin Hausa daga karin maganganun Hausawa idan
har an yarda a yi hakan”. An kuma samar da sakamakon bincike ta hanyar yin
amfani da ihsa’iyar bincike ta “Kashi cikin Ɗari”. Wannan takarda ta gano cewa makaɗa Sa’idu Faru ya kan yi amfani da hikimarsa ya yi zambo
ko habaici ga Sarakuna, da ‘Ya’yansu, da masu riƙe da muƙaman sarauta, da fadawa, da kuma sauran jama’a, don ya
isar da saƙo ga jama’a. Takardar kuma ta gano yawan aukuwar tubalin zambo da
habaici a cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsa. Yayin da
Tubalin zambo ya auku sau kashi 38% cikin ɗar,i shi kuwa, Tubalin habaici ya auku sau kashi 33% cikin ɗari, a cikin waƙoƙin da muka gudanar da nazari a kansu.