Tsakure:
Karin harshen Zamfaranci wani yanki ne daga cikin karin yamma wato Sakkwatanci. Makaɗa Sa’idu Faru mutumin Zamfara ne, ya rayu a wani yanki tun ana haɗe da Sakkwato. Ya yi wa Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Waƙoƙi tun kafin ya zamo Sarkin Musulmi. Manufar wannan muƙala ita ce fito da karin harshen Zamfaranci da aka yi amfani da shi a cikin waƙar “Kana Shire Baban “Yan Ruwa”. An kuma kwatanta shi da daidaitaccen kari domin fayyace ma’anar wasu kalmomin. An yi amfani da hanyar hira da ma’abuta ilimi musamman abin da ya ƙunshi waƙar baka. Haka kuma, an yi amfani da hanyar sauraron wasu daga waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru domin samun hujjojin gina wannan muƙala. An yi amfani da hanyar karance-karancen bugaggun littafai da kundaye da mujallu da muƙalun da aka gabatar domin ƙara wa juna sani, duk domin samun hujjojin da za su gina wannan muƙala. An ɗora wannan maƙala a kan Karin Magana, kamar yadda wasu masana irin su Farfesa Aliyu Muhammad Bunza suka ga dacewar yiwuwar yin haka. Sakamakon haka, an ɗora wannan muƙala a kan karin maganar nan mai cewa: “Kowane Tsuntsu Kukan Gidansu Yake Yi”. Sakamakon wannan bincike ya gano cewa mafi yawan kalmomin da aka yi amfani da su kamar kiyyo, shire da zaka duk na Zamfarci ne, musamman a waƙar “Kana Shire Baban ‘Yan Ruwa”. Ya yi haka ne domin tasirin Zamfaranci da yankin da ya fito.
Fitilun Kalmomi: Makaɗa Sa’idu Faru, Muhammadu Macciɗo, Karin Harshe, Ire-iren Karin Harshe, Zamfaranci
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.028
author/Amina Abubakar, Halima Adamu & Samira Adamu Gurori
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 28