Tsakure:
Ga ɗabi’ar ɗan’adam, tunaninsa da hikimarsa sukan saje da juna da na wani mutum da yake kusa ko kuma nesa da shi. Don haka al’adar ɗan’adam ta tabbatar da haɗuwar ra’ayi ta fuskokin addini ko sana’a ko kuma wani lamari na rayuwa kan haifar da ɗorewar dangantaka ta musamman a tsakanin al’umma. Wannan bincike yana da manufar gudanar da nazari domin ƙyallaro wani abu dangane da samuwar zumunta a wasu daga cikin ɗiyan waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru da kuma na wasu Mawaƙan ƙasar Hausa na fada. Binciken ya yi amfani da hanyoyin da suka haɗa da: Sauraren waƙoƙin baka daga bakin maƙagansu ta hanyar amfani da memori da tuntuɓar wasu masana da suke da masaniya game da waƙoƙin nasu. Haka kuma, nazarin bai kawar da kai ga leƙa wasu wallaffun ayyuka da aka gudanar ba. Ayyukan da aka mayar da hankali a kansu sun haɗa da, wallafaffun matanonin waƙoƙin baka da kuma nazarce-nazarcen da wasu manazarta da ɗalibai suka gudanar. An yi amfani da Bahaushen tunanin da ke cewa: “Da abokin daka akan sha gari” a matsayin hanyar da aka ɗora binciken a kanta. Binciken ya fito da sakamako tare da bayar da wasu shawarwari da za su ƙara wa Borno dawaki. Wasu daga cikin sakamakon da nazarin ya gano su ne: Mawaƙan baka na fada suna amfana da fasahohin junansu inda sukan yi amfani da kalmomi masu alaƙa wajen waƙe iyayen gidansu. Har wa yau, nazarin ya gano cewa, akwai bambanci a tsakanin satar fasaha da waƙeƙeniya da kuma zumuntar fasaha. Binciken ya bayar da shawarar cewa, waɗanda suke da ilimin kwamfuta a cikinmu da su ɓullo da wasu manhajoji da za a riƙa jin muryoyin mawaƙanmu na baka irin su Sa’idu Faru, Salihu Jankiɗi, Ibrahim Narambaɗa da kuma Musa Danƙwairo da Aliyu Ɗandawo Shuni da sauransu da dama.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.016
author/Haruna Umar Maikwari & Ibrahim Dalha
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 16