Tsakure:
Alhaji Sa’idu Faru, makaɗi ne mai bibiyar tsari da yanayi da kuma al’adun sarauta
da masarauta na ƙasar Hausa. Hakan ya sa
yake fito da wasu ɗiya a waƙoƙinsa masu nuna yanayin Sarautar sarakuna da kuma masarauta. A yawancin
lokaci, Sa’idu Faru yakan fito da manya da ƙananan saƙonni waɗanda suka dace da yanayin sarauta da masarauta, musamman a waƙoƙinsa na fada. Manufar
wannan takarda ita ce, fito da yanayin sarauta da masarauta a zubin ɗiyan wasu waƙoƙin Sa’idu Faru. Haka kuma, wannan takarda ta yi amfani da wani ɓangare
na tsarin tarken Waƙar
Baka Bahaushiya (WBB) wato, Gusau (2023) wajen ƙalailaice yanayin sarauta da masarauta, kamar
yadda wannan hanyar nazari ta tanada, sannan kuma an yi amfani da hanyar bi-sharhi,
wato (Qualitative Research). Muhammad (2023) ya
bayyana nau’in bincike bi-sharhi da bincike ne, na
samar da bayanai da suka ƙunshi zurfafa
tunani a kan abubuwa mabambanta. Haka kuma, an tattaro ɗiyan waƙoƙin da aka yi misali da su, daga Diwanin Waƙoƙin Baka na Hausa, wato Gusau (2009) da Kundin Digiri na biyu, wato
(Labaran, 2024). A wannan takarda an yi amfani da irin wannan tsari aka ƙalailaice bayanan da aka samo, wato wasu ɗiyan waƙoƙin Sa’idu Faru da suka danganci yanayin sarauta da masarauta. A wannan
takarda an fahimci Sa’idu Faru yakan
lura da yanayin sarauta da masarauta, musamman ta fito da wasu halaye da
nagartar da sarki ya kamata a ce yana da su a yayin jagorantar al’ummarsa.
Misai, kamar ilimi da kyauta da adalci da iya mulki da faɗar gaskiya da zumunta da iya magana da iya shiga
da sauransu. Haka kuma, an lura da yadda Sa’idu Faru ya nuna yadda girma da bunƙasar
masarauta sukan ƙara
wa Sarki ko sarauta armashi da ɗaukaka
da kwarjini a idon mutane da kuma ƙarfin faɗa
a ji. Har wa yau, an fahimci cewa, duk wani Sarki da ya haɗa waɗannan yanye-yanye na
sarauta da masarauta kamar yadda Sa’idu Faru ya fito da su a zubin ɗiyan wasu waƙoƙinsa, to, zai samu karɓuwa ga talkawansa da sarakuna ‘yan’uwansa da Gwamnati da kuma ƙasa baki-ɗaya. Haka kuma, akasin waɗannan yanaye-yanaye kan rage wa sarki da masarauta daraja da kwarjini a
idanun talakawa da sarkuna ‘yan’uwansa da Gwamnati da ma ƙasa baki-ɗaya.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.017
author/Nura Lawal & Muhammad Rabi’u Tahir
journal/Conference Proceedings | November 2024 | Article 17