Tsakure:
Ga al’ada, idan zama ya haɗa
dole wata rana wani ya yi wa wani laifi har husuma ta shiga. Sanin haka da
Hausawa suka yi, shi ya ba su damar samun hikimar tobassaka, saboda ta rage raɗaɗin
zafin matsalar da zamantakewa za ta iya haifarwa. Wannan dalili ya sa wasannin
taubastaka ha Hausawa ya toshe kafofin tashintashina da fitintunu da dama.
Wannan takarda tana da manufar dubin maganaɗisun
da ke cikin taubastaka na kyautata zamantakewa. Binciken ya yi ƙoƙarin
dubin ayyukan da aka gudanar masu alaƙa da
batun da ake magana a kansa. An yi fashin maƙin a
kan nau’o’in
tobassaka guda goma (10) da aka iya ƙyallarowa. An kwakkwahe bayanan da
aka bayar da wasu ɗiyan
waƙoƙin
baka na Hausa guda huɗu
(4), sai rubutacciyar waƙa guda ɗaya.
Nazarin ya kalli jigogin wasannin taubastaka guda goma (10) inda kuma ya bayar
da misali a kan kowanensu. A ƙarshe nazarin ya gano cewa, Ashe haɗin kan da ke a Nijeriya ta Arewa asali ne gare shi tun a
zumuntar dangogin su da ƙoƙarin haɗin auren zumunta. Yaƙe-yaken da suka wakana tsakaninsu sun
goge miyakunsu da wasannin taubastakar domin Hausawa cewa suke yi: “A share jini a koma wasa.”
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.019
author/Prof. Aliyu Muhammadu Bunza
journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |