Tsakure:
Karin harshe yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantacciyar sadarwa kamar yadda fassara ke da matuƙar muhimmnci a ɓangaren kiwon lafiya, musamman a karkara da ƙauyuka.Wani binciken da aka gudanar ya nuna kashi 77% na ma’aikata da marasa lafiya da ke zuwa Asibitin Ƙwararru ta Yariman Bakura sun fi son amfani da harshen Hausa wajen sadarwa tsakanin marar lafiya da ma’aikatan kiwon lafiya a matakai mabambanta. Har wa yau, daga cikin kashi 77% ɗin kashi 44% sun fi amfani da karin harshen Zamfarci (Bashir & Umar sh. 38, 2024). Wannan dalilin ne ya sa aka yi ƙoƙarin fito da tasirin karin harshen Zamfarci wajen fassara keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura da ke Gusau. An yi amfani da Ra’in Fassara ta La’akari da Karin Harshe, wanda Giles & Johnson (1979) ya yi amfani da shi a aikinsa inda ya nuna yadda ake samun bambancin fassara ta la’akari da karin harshe da kuma waɗanda ake yi wa fassara. Binciken ya gano cewa ana samun bambanci ta fannin fassarar wasu keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya da suka shafi likitancin mata da na ƙananan yara tsakanin daidaitacciyar Hausa da kuma karin harshen Zamfarci ta fuskar tsarin sauti da gundarin kalmomi. Bayan da aka zaƙulo wasu kalmomin kiwon lafiya, aka fassara su tare da bayyana yadda ake faɗin su a Zamfarci, an ba wa ƙwararrun likitoci Zamfarawa domin tantancewa da ba da shawara saboda samun ingantacciyar fassara cikin karin harshen Zamfarci. Sakamakon ya kawo jadawali bakwai na wasu keɓaɓbun kalmomin da suka shafi likitancin mata da ƙananan yara. Ana sa ran a ci gaba da zaƙulo wasu keɓaɓbun kalmomi na wasu sassan kiwon lafiya domin taskace su da samar da wani ƙaramin kundi ko ƙamus na keɓaɓbun kalmomin kiwon lafiya cikin daidaitacciyar Hausa da karin harshen Zamfarci domin ƙara inganta sadarwa musamman a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura da sauran asisibitocin da ke cikin ƙasar da ake amfani da karin harshen Zamfarci.
Fitilun Kalmomi: Kalmomin kiwon lafiya, Karin harshen Zamfarci, Cututtukan ƙananan Yara, Asibiti
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.020
author/Muhammad Arabi UMAR & Abdullahi BASHIR
journal/Tasambo JLLC 3(2) | September 2024 |