Nazarin Rikiɗar Wasu Sautukan Harshen Ngizim Zuwa Hausa

    Tsakure: 

    A duk lokacin da aka samu wata cuɗanya ta mu’amala tsakanin harsuna mabambanta guda biyu, akan samu harshe mafi tasiri a tsakaninsu. Irin wannan dangantaka ta tsakanin harsuna, ita takan sa harshe mafi tasiri ya yi naso har ya kawo wasu sauye-sauye a wani ɓangare na harshe abokin mu’amalarsa mai ƙarancin ƙarfin tasiri. Harshen Hausa da na Ngizim, harsuna ne da suke da ƙullalliyar alaƙa ta asali ɗaya da kuma ta mu’amala bisa tsarin zamantakewa. Manufar wannan bincike ita ce, nazartar irin rikiɗar da wasu sautukan Ngizim sukan yi ta hanyar narkewar furucinsu na asali zuwa wasu na daban a Hausa. Dangane da hanyoyin gudanar da binciken, an yi amfani da dabarar tatsar bayanai daga ‘yan asalin harshen Ngizim ta hanyar sauraron maganganunsu a muhallai daban-daban da kuma karantawa daga wallafaffun littattafai da takardu na masana domin tantancewa da ma kafa hujja a kan bayannan da aka tatsa. Haka nan, Ra’in Tsarin Sauti Ɗan Tsirau (Theory of Generative Phonology) na Chomsky da Halle, (1968) da kuma Ra’in Cuɗanya (Contact Theory) na Uriel Weinreich (1953) su aka yi amfani da su a matsayin ra’in da aka ɗora binciken a kai. Bugu da ƙari, binciken ya gano cewa, wasu keɓaɓɓun sautuka a harshen Ngizim kamar /ə/ da /dl/ da /tl/ da kuma /zh/ suna rikiɗa zuwa wasu sautuka na harshen Hausa sakamakon ƙarfin tasirin da harshen na Hausa ya yi a kan na Ngizim.

    Fitilun Kalmomi: Rikiɗa, Tsarin Sauti, Tasiri, Cuɗanya, Furuci

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i02.002

    author/Sa’adu Inusa

    journal/Tasambo JLLC 4(2) | July 2025 |