Tsakure
Manufar wannan takarda ita ce zaƙulo tasirin da zamani ya yi wa sana’ar. An taƙaita farfajiyar binciken ga cikin birnin Sakkwato kaɗai. Takardar ta yi ƙoƙarin waiwayen wasu daga cikin ayyukan da hannunta ya samu damar kaiwa gare su waɗanda suka haɗa da kundayen bincike da mujallu da kuma littattafai. An yi amfani da hanyoyin bincike na ziyarar gani da ido da hira da tattaunawa. Sauran hanyoyin da aka yi amfani da su sun haɗa da, karance-karance da amfani da wayar hannu da shiga kafar sadarwa ta WhatsApp da kuma ta google. Haka kuma, takardar ta yi amfani da karin maganar Hausawa da take cewa: “Zamani riga” a matsayin hanyar ɗora aiki. Binciken ya yi ƙoƙarin dubin sana’ar ɗinkin hannu a jiya da kuma yadda take a yau. Hakan ya sa aka fayyace ɗabi’un masu sana’ar da kuma yadda ake koyon ta. Binciken ya ƙyallaro wasu daga cikin alfanun tasirin da zamani ya yi wa sana’ar ɗinkin hannu da kuma illolin da ya haifar mata. Wasu daga cikin abubuwan da takardar ta gano sun haɗa da, duk da tsawon lokaci da sana’ar ɗinkin hannu ta ɗauka a ƙasar Hausa, har yanzu abubuwan da take samarwa na adon riguna (sutura) suna da tagomashi a idon tsofaffi da matasa.
Fitilun Kalmomi: Sana’a, Zamani, Ɗinki, Ɗinkin Hannu
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i02.001
author/Ibrahim Dalha
journal/Tasambo JLLC 4(2) | July 2025 |