Tsakure:
Ilimi shi ne ginshiƙin rayuwa, kuma a matakin fako na neman ilimin wato makarantar firamare, a nan ne ake fara ɗora yara bisa hanya na koyon karatu da kuma fahimtar abin da ake koya masu. Saboda haka, amfanin harshen Uwa baya ga harshen Ingilishi abu ne mai muhimmanci domin kuwa yana agazawa wajen sanya yara su fahimci saƙon da malami ke son isarwa gare su, kuma yakan taimaka wajen sanya su, su fahimta cikin ƙanƙanin lokaci. Saboda muhimmancin harshen uwa wajen koyo da koyarwa a makarantun Firamare yasa hukumar tsare-tsaren ilimi ta ƙasa ta amince da yin amfani da harshen Uwa wajen gudanar da koyarwa a makarantun. Wannan bincike ya fito da sababbin dubarun amfani da harshen Uwa tare da harshen Ingilishi wajen Koyar da yara tun daga matakin farko har zuwa mataki na shida. Saboda muhimmancin amfani da harshen Uwa Wajen Koyarwa a makarantun Firamare, ya sanya ƙungiyoyi masu zaman kansu, suka yiwo hoɓɓasa wajen bayar da tasu gudummuwa domin cimma nasarar wannan buri, ƙungiyoyi irin su: Better Education Service Delivery for All (BESDA) sun ɗauki nauyin buga littafin RANA tare da haɗin guiwa da hukumar ilimi na matakin farko na Jihar Kaduna (Universal Basic Education) da kuma taimakon Bankin Duniya (World Bank). Sannan akwai ƙungiyar USAID na mutanen ƙasar Amurka wanda suka buga littafin Early Grade Reading na Hausa kuma mu karanta domin agazawa wannan manufa na tsare-tsaren ilimi na ƙasa kai ga samun nasara. Wannan bincike zai kalli ire-iren gudummuwar da waɗannan littattafai suke bayarwa tare da kawo sababbin hanyoyi da za su taimaka wajen bunƙasa amfani da harshen Uwa wajen koyarwa a matakan ilimin firamare.
Fitilun Kalmomi: Harshen Uwa, Ilimi, Koyo Da Koyarwa, Makarantu Firamare
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i02.005
author/Abubakar Yakubu & Dalhat Ahmad Mustapha
journal/Tasambo JLLC 4(2) | July 2025 |