Tsakure:
A Bahaushiyar al’ada, rayuwar al’umma ta ta’allaƙa ne a kan abubuwan da suke gudana na yau da kullum, waɗanda suka shafi al’adu da tadodi da suke wakana a tsakaninsu. Daga cikin irin waɗannan al’adu akwai waɗanda suka danganci magani. Kasancewar lamarin magani da warkarwa wani fanni ne na rayuwa mai matuƙar muhimmanci, ya sa a duk wata harka da Bahaushe zai yi a rayuwa sai an sasmi nason magani a ciki. Mata a nasu ɓangaren su ma ba a bar su a baya ba domin kuwa suna kallon taimako ko asiri na magani a matsayin ɗaya daga cikin sigar zamantakewarsu. Don haka, neman magani da yarda da shi a tsakanin mata tamkar wani abin dogaro ne a gare su. Manufar wannan muƙala shi ne ta fito da magungunan da mata ke amfani da su wajen waraka. Sai kuma waiwayen wasu ayyuka na masana masu alaƙa da binciken a taƙaice. An ɗora wannan aikin a kan ra’in tabbatuwar magani wanda Premeswari, Hibino da Koyama (2016). suka ƙirƙiro, a inda suka bayyana cewa wasu magungunan akan yi la’akari da shekaru, jinsi, nahiya ko kuma launin fata. Haka kuma kowanne rukunin mutane a cikin wata al’umma suna da wasu al’adu da suke yi wanda ya bambanta su da rukunin da yake a same su ko a ƙasa da su. Haka kuma takardar ta yi bayanin magani da amfani da shi domin waraka daga wasu cututtuka na mata, waɗanda suke da alaƙa da mahaifa kamar su al’ada da biki da kafewar/toshewar mahaifa da warin gaba da sauransu. An yi nasarar gano cewa, matan Hausawa kan yi amfani da magungunan gargajiya wajen gyaran jikinsu fiye da magungunan zamani. Haka kuma al’ummar Hausawa har yanzu sun fi gamsuwa da wasu magungunan gargajiya wajen samun waraka.
Fitilun Kalmomi: Magani, Magungunan Mata, Gyaran Jiki, Magungunan Gargajiya
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i02.004
author/Zalihat Ammani PhD
journal/Tasambo JLLC 4(2) | July 2025 |