Tsakure:
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin rawar da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta taka a Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin soja a karo na biyar a cikin tarihin ƙasar. Haka kuma, an amfani da hanyar bibiyar wasu ayyukan da kuma kafofin yaɗa labarai domin tattaro bayanan wannan bincike. A sakamakon wannan bincike an lura a ci gabanta na ayyukanta sun faɗaɗa zuwa kiyaye tsaron yankin kuma ECOWAS, ta samu nasarori wajen shiga tsakani game da juyin mulki da rikici da dama da aka samu a mambobin ƙungiyar. Bayan da juyin mulkin Nijar karo na biyar ya faru, ECOWAS ta ƙoƙarta wajen shiga tsakani. Ta tura tawagar diflomasiyya don gudanar da tattaunawa ta siyasa, kuma ta saka takunkumin tattalin arziki kan Jamhuriyar Nijar. Haka kuma, tana tattaunawa kan yunƙurin tura sojoji domin daƙile juyin mulkin soja karo na biyar a tarihin Jamhuriyar Nijar a ƙarƙashin shugabancin shugaban karba-karba Shugaban Najeriya Ahmed Bola Tinubu. Amma dukkan matakan da aka ɗauka ba su haifar da sakamako masu kyau ba, kuma ECOWAS ta canja matsayinta daga ƙoƙarin sasantawa zuwa sassautawa. Gazawar ƙungiyar ECOWAS don shiga tsakanin juyin mulki na Jamhuriyar Nijar ta nuna kasawar ƙungiyar ECOWAS wajen daidaita manyan batutuwan yammacin Afirka da kuma saɓani a tsakanin mambobinta. A shekaru nan an samu yawan juyin mulki a yammacin Afirka, wannan matsala tana kuma dinga ƙaruwa. Shi ya sa akwai dimbin muhimmanci don a yi bincike mai zurfi kan dalilin gazawar shiga tsakani ta ECOWAS. A wannan kundi, an yi nazari bisa ra’ayin kasancewar ɓangarori daban daban ta hanyar binciken ayyukan manazarta da aka rubuta, da nazarin tarihi da sauransu, tare da fito da hujjar ƙungiyar ECOWAS ta yi sassautawa bayan sassantawar juyin juya mulkin Nijar.
Muhimman Kalmomi: ECOWAS, Shiga Tsakani, Juyin Mulki, Sasantawa
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i01.003
author/Pengcheng Li & Nura Lawal
journal/Tasambo JLLC 5(1) | February 2026 |




