Tsarin Shugabanci a Sana’ar Wayar Hannu (Handset) a Kasuwar Famsenta, Birnin Kano

    Tsakure: 

    Wannan takarda ta yi duba ne a kan yadda tsarin shugabanci yake a kasuwar Famsanta da ke Kano inda ake hada-hadar wayar hannu ko salula (Handset). Babu shakka shugabanni ko ƙungiyoyin wannan kasuwa suna taka rawar gani wajen tafiyar da harkokinsu na sana’ar waya yadda ya kamata, musamman wajen samar da haɗin kai da samun sabbin kayayyakin gyare-gyaren wayoyi na zamani waɗanda suke inganta sana’arsu da su. Yayin tattaro bayanai na wannan bincike, an tattauna da shugabannin wannan kasuwa ta Famsanta da su waɗanda ake jagoranta domin samun ingantaccen bayanai daga gare su, haɗi da kuma karance-karance. Haka kuma, an yi amfani da ra’in Shugabancin Sauyi (Transformational Leadership Theory) wajen gudanar da binciken. Daga ƙarshe, binciken ya gano cewa tsarin shugabanci yana matuƙar taimakawa masu sana’ar wayar hannu da ke kasuwar famsanta yayin gudanar da hada-hadarsu ta sayar da waya da gyare-gyaren waya da ma sayar da kayayyakin waya, musamman ta fuskar samun sababbin kayayyaki na zamani na abin da ya sh*afi wayar hannu wanda hakan kan kawo wa sana’arsu ci gaba.

    Fitilun Kalmomi: Shugabanci, Sana’a, Wayar Hannu, Kasuwar Famsenta, Birnin Kano, Ƙungiya

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i01.001

    author/Nasir Usman Nasir & Jabiru Barau 

    journal/Tasambo JLLC 5(1) | February 2026 |