By
Hamza Gambo
Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya
Jami’ar Bayero Kano
Email:
hgambo.hau@buk.edu.ng
Da
Khadija Auwal Bala
Da
Hafsat Ɗahiru Musa
Tsakure
Wannan
nazari an aiwatar da shi ne a kan fayyace salo a sharhin wasannin ƙwallon ƙafa na Abubakar Isa
Dandago ya gabatar a wasan Machester United da Galatasari da kuma wasan Kano
Pillars Sai masu Gida da Gombe United. Nazarin an aiwatar da shi ne ta hanyar
samo bayanai daga gidajen rediyo da ɓidmid da kuma kafafen sada
zumunta kamar facebook da tiktok, haka kuma an tattatuna da mai sharhin
wasanni. An gudanar da nazarin wannan takarda ta bin bayanan da masani Farfesa
Sa’id Muhammad Gusau ya samar (2015) ya kawo na aiwatar da nazarin salon
sarrafawa a cikin waƙa, an kuma yi amfani da matakan da mazhabar ta samar na
nazarin dabarun jawo hankali. Manufar wannan takarda ita ce gano adon harshe da
aka yi amfani da su a sharhin wasannin ƙwallon ƙafa da aka aiwatar da
harshen Hausa, ta hanyar kafa hujjoji daga bayanan da aka samo daga kafafen
sadarwa. Sannan aka yi sharhin dukkannin abubuwan da nazarin ya gano. A ƙarshe binciken ya
gano adon harshe a sharhin wasannin kwallon ƙafa na Hausa, ta
hanyar fayyace saƙon da bayanai da ke ɗauke da shi daki-daki.
Fitilun
Kalmomi: Adon
harshe, ƙwallon ƙafa, Hausa
DOI: www.doi.org/10.57233/tjllc.2026.v06i01.005
author/Hamza Gambo & Khadija Auwal Bala & Hafsat Ɗahiru Musa
journal/Tasambo JLLC 6(1) | December 2026 |




